• Home  
  • Hisbah A Jihar Katsina Ta Lalata Barasar Naira Miliyan 60
- Babban Labari - Labarai

Hisbah A Jihar Katsina Ta Lalata Barasar Naira Miliyan 60

Dakarun Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, sun lalata barasa da ƙwayoyi da ta ƙwace da kuɗinsu ya kai kimanin Naira miliyan 60 a Ƙaramar Hukumar Funtua da ke jihar Katsina. Dokta Aminu Usman Kwamandan Hisbah na jihar Katsina ne ya sanar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN). Dokta Aminu ya ce, hukumar ta […]

Dakarun Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, sun lalata barasa da ƙwayoyi da ta ƙwace da kuɗinsu ya kai kimanin Naira miliyan 60 a Ƙaramar Hukumar Funtua da ke jihar Katsina.

Dokta Aminu Usman Kwamandan Hisbah na jihar Katsina ne ya sanar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN).

Dokta Aminu ya ce, hukumar ta ƙwace  giya kwalaye 1,750 da jarkoki 33 da aka sarrafa su a cikin Funtua.

Kwamandan ya jinjina wa ma’aikatan hukumar kan ƙoƙarinsu, ya kuma buƙaci su matsa kaimi wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Kwamandan na Hisbah a jihar Katsinaa ya roƙi shugabannin Addini a jihar da su tallafa wa hukumar, inda ya ce Hisbah ta kowa ce ba ta da gefe.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000