A ranar Talata 7 ga watan Nuwamban shekarar 2023 aka yi jana’izar mai girma Magajin Rafin Hadejia, Alhaji Mohammadu Babandede Sarkiki, mahaifi ga Muhammad Babandede, Tsohon Shugaban Hukumar Shigi Da Fici Ta Kasa.
Dubban mutane daga ciki da wajen jihar Jigawa ne suka halarci jana’izar, har da gwamnan jihar Alhaji Umar Namadi Danmodi.
Al’umma gaba ɗaya sun nuna alhininsu tare da addu’ar Allah Ya gafarta masa. Amin.
A Hannun Dama: Lokacin da jirgin sama ya sauka da gawar Magajin Rafin Hadejia a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a ranar Talata 7 ga watan Nuwamba bayan rasuwarsa a birnin AlKahira, kasar Masar a ranar Lahadi 5 ga watan Nuvamba da daddare.