Ƙungiyar Shirya Fina-finanai a Harsunan Nahiyar Afirika ta KILAF ta karɓi baƙuncin Hukumar Ƙirƙirar Da Fasaha Ta Najeriya (National Gallery of Arts) domin ƙara ƙarfafa alaƙar da take tsakani.
Tattaunawar su ta mayar da hankali ne wajen taron da KILAF ɗin za ta shirya a ranar 25 zuwa 30 ga watan Nuwamban shekarar, 2024.
Ana sa ran taron zai gudana ne a babban ɗakin taro na Ado Bayero dake Kano, inda za’a baje kolin kayayyaki da kuma shirye-shiryen da suka shafi al’adu.
- Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika Taci Tarar Kasar Libya Makudan Kudade Akan Abin da Sukayiwa Super Eagles.
- Sanata Barau Ya Jajantawa Al’ummar Jigawa
Bakin sun samu tarba ta musamman daga babban daraktan KILAF Alhaji Abdulkareem Muhammad

