Hukumar shigi da fici ta Najeriya reshen jihar Kano ta yi bikin karawa jami’anta 450 girma a jiya Alhamis 10 ga Satumbar, 2024.
Daga cikin jami’an da hukumar ta karawa girma su 450, akwai manya 307 yayin da wasu masu kananan mukamai 114 suka samu matsawa mukamai na gaba.
Mataimakin kwampturola HM Tahir mai kula da sashen ma’aikata na hukumar “Immigration” reshen jihar Kano ya bayyana cewa ba iya karawa jami’an girma aka yi ba, a a wani yunkuri ne na yabawa da aikin da suke yi ne da kuma halin sadaukarwa da suka nuna.
“Wannan karin girma ba iya yana wa aiki tuƙuru da kuke yi ba ne, ac wannan wata shaida ce da ke nuna yabawa da sadaukarwar da kuke yi,
“Alama ce ta ƙwarewarku, da himma wurin tabbatar da cigaban hukumar shige da fice.
- Sarkin Musulmi Ya Roƙi ‘Yan Najeriya Su Cigaba Da Yiwa Shugabanni Addu’a.
- Ya Kamata A Cire Rigar Kariya Ga Shugabanni-Sheikh Pantami
“Muna yabawa yadda kuka jure ƙalubale masu sarƙaƙiya, ku ka tabbatar da tsaro iyakokinmu, da kuma taimakawa waɗanda ke neman sabbin damammaki a ƙasarmu.
Taron ya gudana ne a shedikwatar hukumar da ke nan Kano a safiyar jiya Alhamis.
Daga cikin wadanda su ka samu halartar taron, akwai shugaban hukumar Civil defence, da shugaban hukumar gidajen hari na jihar Kano. Da kuma ‘yan uwa da abokan arzikin jami’an da aka yi bikin ƙarawa girma.