Hukumar Kiyaye Hadura Ta Tabbatar Da Mutuwar Tawagar Yan Wasan Kano 21

Hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar Kano,( FRCN)  ta tabbatar mutuwar mutane 21 yayin da mutane 11 suke asibiti don samun kulawar likitoci, sakamakon mummunan hadarin da ya faru da tawagar yan wasan Kano, bayan kammala halattar gasar wasanni ta kasa (NSF) da aka gudanar a jihar Ogun, inda motarsu ta fada kasan wata Gada a yankin Dakatsalle karamar hukumar Kura, kan hanyarsu ta dawo wa gida yau asabar.

Kakakin hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar Kano, CRC Abdullahi Aliyu Labaran, ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai.

Sanarwar ta ce bayan samun mummunan labarin jami’ansu sun garzaya inda lamarin ya faru , tare da kai wadanda suka jikkata asibitin kwararru na Murtala Muhammed da kuma gwawarwakin.

Hukumar ta mika sakon ta’aziyarta ga gwamnatin jihar Kano da iyalan mamatan harma da al’ummar jihar baki daya kan iftila’in hatsarin motar da yayi sanadiyar rasuwar matasan tare yin addu’ar samun lafiya ga wadanda suka jikkata.

Haka zalika hukumar ta yi kira ga al’ummar jihar Kano dama masu ababen hawa da su dinga kiyayewa da dokokin tuki a koda yaushe.

 

Post masu alaƙa

Barista Hamza Ɗantani ya jinjinawa CP Bakori da wasu kwamishinonin yan sanda biyu.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ceto fasinjoji 9 bayan musayar wuta da yan bindiga a hanyar Doguwa.

Jigawa ta kaddamar da tsare-tsaren bunƙasa kananan hukumomi 27 na shekaru biyar.