20 Daga Cikin Tawagar Yan Wasan Kano Sun Rasu Akan Hanyar Dawo Wa Gida

Akalla mutane 20 daga cikin tawagar Jihar Kano, sun rasu,yayin da wasu suka samu munanan raunuka, sakamakon fadawar motarsu kasan wata Gada a Dakatsalle dake karamar hukumar Kura, a kan hanyarsu ta dawo wa gida bayan kammala halattar gasar wasanni ta kasa (NSF) da aka gudanar a jihar Ogun.

Rahotanni na cewa motar tana dauke da mutane 35 kuma ta yi hatsarin ne da safiyar yau asabar

Shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano, Umar Bala Fagge, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce motar tana dauke da mutane 30.

Sai dai ya ce mutane 19 ne suka rasu kamar yadda suka lissafa.

Haka zalika tsohon mataimakin shugaban marubuta wasanni ta jihar Kano (SWAN) Ado Salisu, ya bayyana kaduwarsa tare da cewa an kai wadanda suka jikkata asibitin gwamnati dake karamar Kura

Har zuwa lokacin wallafa wannan labarin hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar Kano, ta fitar da karin bayani ba kan faruwar lamarin amma dai manema labarai sun aike da neman karin bayani ga hukumar.

 

Post masu alaƙa

AIG Garba Ahmed ya karrama sabon kwamishinan yan sanda CP Taiwo a Kano.

Yan sandan Kano sun miƙa wa masu su motoci biyu da suka ƙwato tare da kama mutum Daya da ake zargi.

Bene mai hawa daya da ake ginawa ya rushe a jihar Sokoto