Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce taba sigari tana kashe rabin masu shanta a fadin duniya.
Mutum milyan shida ke mutuwa saboda shan taba sigari, inda kuma 900,000 ke mutuwa saboda shakar hayakinta.
Manufar bikin shine yaki da shan taba sigari da mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a game da hadarin da ke tattare da shan taba sigari da lalubo hanyoyi da dabarun kare kananan yara masu tasowa daga fadawa cikin masu shan taba sigari.
Taken bikin na wannan shekarar shine haskaka illolin da taba sigari, nicotine da masana’antu masu alaƙa da ake amfani da su don jawo hankalin sabbin masu amfani da su – musamman matasa.
- 20 Daga Cikin Tawagar Yan Wasan Kano Sun Rasu Akan Hanyar Dawo Wa Gida
- Yan Sanda Sun Gurfanar Da Wanda Ake Zargi Da Satar Sarkar Karfe
Wannan batu ne mai matukar muhimmanci da zai wayar da kan al’umma da janyo hankalin gwamnati da masu ruwa da tsaki don kare yara daga fadawa shan taba sigari ta hanyar wayar da kan jama’a da bayar da shawarwari kan illar da ke tattare da hakan.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa sama da mutane Miliyan bakwai ke mutuwa a duk shekara sanadin matsalolin da suka danganci shan taba sigari, kuma tana kawo koma baya ga tattalin arzikin kasashe
Yau ranar 31 ga watan Mayu, rana ce da aka kebe domin yaki da shan tabar sigari a duniya, saboda haka hukumar lafiya ta duniya ta yi kira ga gwamnatoci da su ‘dauki kwakkwaran matakan shawo kan matsalar shan taba sigari, domin kare lafiyar mutane da kuma tattalin arzikin kasashen.
Hukumar WHO wadda ta baiyana taba sigari a matsayin barazana ga ci gaba. Baya ga kashe sama da mutane Miliyan bakwai a duk shekara. Hukumar lafiya ta duniya ta ayyana sigari a matsayin annoba kuma daya daga cikin cututtukan da duniya ba ta taba ganin irinsu ba.
Ga wasu daga cikin illolin da sigari ke yiwa mai shan sa:
- Shan sigari na haddasa mutuwar mutane miliyan shida a kowace shekara.
- Sigari shine abu na biyu a ke haddasa mutuwa sannan abu na hudu da ke haddasa cututtuka a fadin duniya.
- Sigari na da sinadaran kemikal sama da 7,000 a hayakinsa. Akalla guda 250 na da illa, daga cikin wdannan 69 na hafar da cutar kansa. 4. Sigari na da illa ga garkuwan jikin dan Adam.
- Sigari ne sanadiyar munanan cututtuka sama da 25 da sukahada da hawa jini, ciwon zuciya, kansa, asma, rubewar hakora, rashin aihuwa, gyambon ciki da sauransu.
- Sigari na haifar da matsaloli ga masu juna biyu. 7. Shan sigari na kawo kansar makokwaro.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce a yanzu akwai ƙasashe 151 da ke da dokokin haramta shan taba sigari a wuraren taruwar jama’a.
WHO ta ce waɗannan dokoki suna kare kusan mutum bakwai daga cikin 10 faɗawa shan ntaba a duniya, sakamakon shan sigarin da wasu ke yi.