Hukumar NOA ta bayyana damuwarta kan masu boye kayan abinci a watan Ramadan.

Babban Daraktan Hukumar wayar da kan ƴan Najeriya wato National Orientation Agency (NOA), Mallam Lanre Issa-Onilu, ya gargaɗi ga ƴan kasuwa, a faɗin ƙasar nan da su guji ɓoye kayan masarufi ko ƙara farashi ta hanyar  don cin kazamar riba a wannan wata na ramadana.

Mallam Issa-Onilu ya nuna damuwa kan rahotannin  cewa wasu ƴan kasuwa na ɓoye muhimman kayan abinci da aka fi amfani da su a lokacin azumi, lamarin da ke haifar da ƙaranci a kasuwa tare da tashin gwauron zabi na farashi, abin da ke cutar da talakawan Najeriya.

Ya ƙara da cewa ɓoye kayan abinci da gangan na kawo cikas ga ƙoƙarin da ake yi na daidaita tattalin arziki, yana ƙara hauhawar farashi tare da jefa iyalai cikin ƙangin wahala.

Haka kuma, ya buƙaci ƙungiyoyin ƴan kasuwa, da sauran ƙungiyoyi da su sanya ido kan mambobinsu tare da hana duk wata dabi’a tsawwala, Ya kuma nemi haɗin kai da hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da bin ƙa’idojin kasuwanci na gari.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda