Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen Jihar Sakkwato, ta kama tan 3.9 na miyagun ƙwayoyi tare da cafke mutum 599 cikin shekarar da ta gabata.
Kwamandan hukumar a jihar, Mustapha M. Gidado ne, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka shirya domin bikin Ranar Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi ta Duniya ta 2026.
A cewarsa, daga cikin waɗanda aka kama akwai maza 532 da mata 67, yayin da kotu ta yanke wa mutum 24 hukunci, sauran shari’u 33 kuma na ci gaba da gudana.
Ya ce miyagun ƙwayoyin da aka ƙwato sun haɗa da: tabar wiwi mai nauyin tan 1.2, magungunan ƙwayoyi masu sa maye masu nauyin kilogram 127.5 da kuma tan 2.5 na sinadarin codeine.
Gidado, ya ƙara da cewa mutum 65 sun samu kulawa da gyaran hali saboda matsalar shaye-shaye, yayin da sama da mutum 200 suka amfana da shirye-shiryen ba da shawara.
Ya buƙaci iyaye, shugabannin al’umma da matasa su riƙa ba wa NDLEA bayanai kan masu safarar miyagun ƙwayoyi domin taimakawa wajen yaƙi da wannan matsala.