Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta Najeriya ICPC ta fara bin diddigin wasu ayyuka na Naira miliyan dubu 21 a fadin jihar Kaduna.
Hukumar ta ce wannan matakin na daga cikin kokarinta na tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen gudanar da ayyukan da ake yi da kuɗaɗen jama’ar Najeriya.
Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, babban Sufeton ICPC, Haruna Aminu, wanda ya wakilci sashen bin diddigin hukumar da ke karkashin jagorancin Dakta Musa Adamu Aliyu, ya ce hukumar na bibiyar ayyuka 60 a fadin jihar Kaduna.
“Mun zo nan ne domin bin diddigin ayyuka kusan 60 a fadin jihar Kaduna da suka laƙume Naira biliyan 21.
“Mun fara wannan aiki a ranar Laraba da yankin Kafanchan, inda muka binciki akalla ayyuka 21.
“Yanzu haka muna bibiyar ayyukan da ake gudanarwa a cikin birnin Kaduna, a unguwanni kamar su, Kabala.
“Aikin namu ya mai da hankali kan ayyuka irin su fitulun titi mai amfani da hasken rana.
- Ciyaman Ɗin Kabo Ya Saya Wa ‘Yan Gabasawa Filin Maƙabarta
- Sanata Barau Ya Bai Wa ‘Yan Sanda Babura Dubu 1 A Kano
Ya kuma ce hukumar za ta yi amfani da dabaru domin matsawa ‘yan kwangilar da aka ba ayyukan ƙaimi su kammala ayyukan.
babban Sufeton ICPC, Haruna Aminu ya bayyana cewa babu wani dan kwangila da za a ragawa, ba za su bari a karbi kudin gwamnati a tafi ba tare da kammala ayyuka ba.
Ya kuma ce zamanin yin watsi da aiki ya wuce domin an ba su dukkan goyon bayan da suke buƙata domin tunkarar duk wadanda suka kasa kammala ayyukan da aka basu.
Aminu ya ce mataki na gaba shine kama ‘yan kwangilar da suka kasa gudanar da ayyukansu, domin tabbatar da cewa ‘yan kasa sun samu ribar dimokuradiyya.