Iran ta ce ba za ta buɗe Hormuz ba har sai Amurka ta cika sharuɗɗan yarjejeniya

Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya sake jaddada cewa Iran ba za ta buɗe Mashigar Hormuz ba har sai Amurka ta aiwatar da dukkan sharuɗɗan da ke cikin yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin ƙasashen biyu.

Qalibaf ya ce Iran na buƙatar a cire takunkumin da aka ƙaƙaba mata, a saki ƙadarorinta da aka ƙwace, a kawo ƙarshen takunkumin man fetur, tare da dakatar da duk wata barazanar soja kafin a buɗe mashigar.

Ya kuma yi gargaɗin cewa Iran a shirye take ta mayar da martani mai tsanani idan aka sake kai mata hari.

Kalaman nasa sun zo ne bayan jami’an Rundunar Juyin Juya Halin Iran sun bayyana irin wannan matsayi, yayin da wa’adin kwanaki 60 da yarjejeniyar ta tanada ya ƙare ba tare da cimma cikakkiyar yarjejeniyar ba.

A nasa ɓangaren, shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba ya sha’awar tsawaita yarjejeniyar wucin gadi da Iran.

Post masu alaƙa

Shugaban Chadi Mahamat Deby zai yi wa wasu da aka ɗaure afuwa

Dole al’umma su taka rawa wajen daƙile yaɗuwar Ebola – CDC

Afirka ta Kudu na fuskantar ƙarancin ma’aikata bayan ficewar baƙi saboda ƙin jini