A mako guda, Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama mutum 80 tare da watsa maboya 16 na masu ta’ammali da miyagun kwayoyi a Jihar Kano.
Hukumar ta fara samamen, mai suna “Operation Restore Order” ne daga ranar 10 zuwa 16 ga watan nan na Agusta, inda ta kai farmaki a matattarar ’yan kwaya a wasu unguwanni.
Yankunan da aka yi kamen sun hada da Filin Mahaha, Koki, Dorayi, Rijiyar Lemo, Charanchi, Kasuwar Kurmi, Zage, Gwammaja, Sauna, Wambai, Yan Ayaba, Indabawa, Kauyen Bela, Farm Centre, Masaka and Panshekara.
Miyagun kwayoyin da aka kama a hannunsu sun hada da tabar wiwi, kwayoyin Diazepam da Exol-5, gam din shalisho da sauransu da kuma makamai.
Kwamandan Sashen Dabaru na NDLEA a Kano, CN DY Lawal, ya ce hukumar za ta ci gaba da matsa kaimi a wuraren taruwar masu ta’ammali da miyagun kwayoyi da hana sake taruwar bata-garin da aka tsarwatsa.
Ya gargadi masu ta’ammali da miyagun kwayoyi da su shiga taitayinsu, saboda Hukumar NDLEA ba za ta raga wa duk wanda ya shiga hannu ba.
CN Lawal ya ce za a gurfanar da mutanen da aka kama bayan an kammala bincike, a yayin da hukumar take ci gaba da bincike da nufin ganowa da toshe manyan hanyoyin safarar miyagunk kwayoyi.
Don haka ya roki jama’a da su goyi bayan gangamin Hukumar NDLEA na yaki da miyagun kwayoyi tare da taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanai domin samun nasara