Sojojin ƙasar Isra’ila sun ce sun kai wasu hare-hare ta sama gabashin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Rundunar sojin ta ce wannan hari wani yunƙuri ne na cika alkawarin da ta dauka na mayar da martani kan harin da Iran ta kai mata a baya.
Harin na kai tsaye ya haifar da fargaba da tashe-tashen hankula.
Ana fargabar ɓarkewar mummunar tarzoma a yankin Gabas ta Tsakiya n
da ka iya rikidewa zuwa yakin basasa tsakanin Isra’ila da Iran.
Wani jami’in Amurka da ya nemi a sakaya sunansa ya ce Isra’ila ta sanar da jami’an gwamnatin Biden aniyar kai harin.
Jaridar NewYorkTimes ta bayyana cewa Jami’an Fadar White House da na Pentagon sun tuntubi Isra’ila a ‘yan kwanakin nan kan nau’in harin da Isra’ila za ta kai wa Iran.
- Za A Fara Hukuncin Ɗauri Ga Masu Ƙin Saka ‘Ya’yansu A Makaranta A Najeriya
- Babu Ranar Daina Amfani Da Tsoffin Takardun Naira” – CBN
Jami’an Ƙasar Amurka sun bayyana rashin jin daɗinsu ga Ƙasar Isra’ila saboda rashin yi wa fadar Washington bayani gabanin harin ta da ya yi sanadiyar mutuwar shugaban Hizbullah, Hassan Nasrallah.
A halin yanzu dai ɗarurruwan Iraniyawa ne ke bayyana ra’ayoyinsu kai tsaye a kafafen sada zumunta dangane da harin.