Rundunar ’yan sandan Jigawa ta raba tallafin Naira miliyan 31 ga iyalan jami’anta 59 da suka rasa rayukansu a bakin aiki.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, inda ya bayyana cewa wannan mataki na nuna irin ɗawainiyar da rundunar ‘yan sandan ke yi wajen kula da jin daɗin jami’anta da iyalansu.
Aminiya ta ruwaito cewa Kwamishinan ‘yan sandan Jigawa, CP Dahiru Muhammad ne ya wakilci Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, wajen raba tallafin a ƙarƙashin shirin nan na tallafa wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka mutu a bakin aiki wato Group Life Assurance (GLA) da kuma IGP Family Welfare Scheme.
Da yake miƙa tallafin, CP Dahiru ya bayyana jami’an da suka rasu a matsayin “jarumai da suka sadaukar da rayukansu wajen kare al’umma domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kan ƙasa.”
- Rikicin Adawa Da Cin Zaben Shugaba Paul Biya Ya Bazu A Kamaru
- Majalissar Dattawan Nijeriya Zata Tantance Sabbin Hafsoshin Tsaro A Ranar Laraba
Ya ce ba za a taba mantawa da gudummuwarsu ba, yana mai jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da tallafa wa iyalansu domin rage raɗaɗin rashinsu.
Ya kuma shawarci iyalan mamatan da aka rabawa tallafin da su yi tattalin kuɗaɗen wajen ci gaban iyalansu.
A nasa jawabin, wanda ya wakilci iyalan waɗanda abin ya shafa, Malam Surajo Shehu, ya miƙa godiya ga Sufeto Janar da kwamishinan ‘yan sanda na Jigawa bisa wannan kulawa da jinƙai da suka nuna, tare da alƙawarin amfani da kuɗaɗen domin karrama jaruman jami’an da suka rasu.