Ziyarar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya kai birnin Brussels a wannan mako ta nuna wani sabon yunƙuri na Gwamnatin Tarayya wajen faɗaɗa abokan hulɗarta a fannin tsaro, domin rage dogaro da Amurka kaɗai.
Najeriya, ƙasar da ta fi kowacce yawan jama’a a Afirka, na fuskantar ƙalubalen tsaro da dama. Daga ciki akwai rikicin ta’addanci daga masu iƙirarin jihadi a Arewa maso Gabas, sai rikicin makiyaya da manoma a Arewa maso Tsakiya, da kuma rikicin ‘yan aware a Kudu maso gabashin ƙasar.
Tabarbarewar tsaro a yankin Sahel, ya ba ƙungiyoyin ta’adda damar faɗaɗa ayyukansu zuwa yankin Arewa maso Yammacin Najeriya wanda ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Idan ba a manta ba, a ranar 25 ga Disamba, Amurka tare da haɗin gwiwar hukumomin Najeriya ta sanar da cewa ta kai wasu hare-hare a Jihar Sakkwao, tana mai alaƙanta hakan da ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga a yankin.
Haka kuma, a farkon wannan makon ne Rundunar Sojin Amurka ta Afirka (Africom) ta turo sojoji kimanin 100 zuwa Jihar Bauchi, inda ta ce za a ƙaro wasu 100 nan da makonni masu zuwa.
Sai dai Hedikwatar Tsaron Najeriya DHQ ta bayyana cewa an turo sojojin ne bisa la’akari da taimakon da gwamnatin Najeriya ta nema daga Amurkan domin horaswa, tallafin fasaha da kuma musayar bayanan sirri, ba don shiga yaƙi kai tsaye ba.
Haɗin gwiwa da Turai da Turkiyya
A tattaunawar da aka yi ranar Larabar da ta gabata a Brussels, Najeriya da Tarayyar Turai sun amince da ƙarfafa haɗin gwiwa kan zaman lafiya a yankin da yaƙi da ta’addanci.
Kan hakan ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi Firaministan Jamus, Friedrich Merz, da ya tallafa da tsofaffin jirage masu saukar ungulu domin ayyukan sintiri da leƙen asiri a yankin Sahel.
Wani jami’in diflomasiyyar Tarayyar Turai a Abuja ya ce ƙungiyar mai ƙasashen 27 na son ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da Najeriya, musamman a Arewa maso Yamma, tare da samar da kayan aikin soja marasa haɗarin kisa, amma ba za ta tura sojoji ba.
Ya ƙara da cewa Tarayyar Turai ta fi Amurka “tsayawa kan alƙawari, mutunta ikon ƙasa, da bin tsari.”
A watan Janairu da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya kai ziyara Turkiyya wadda ita ce karo na farko cikin shekaru tara da wani shugaban Najeriya ya kai can, inda aka tattauna kan haɗin gwiwar tsaro.
Shi ma kuma Jakadan Turkiyya a Najeriya, Mehmet Poroy, ya ce kamfanonin ƙasarsa za su samar da kayan aikin soja da muhimman na’urori, tare da yiwuwar haɗin gwiwa wajen sarrafa wasu kayayyaki a cikin Najeriya.
Turkiyya dai na daga cikin manyan ƙasashen da ke fitar da jiragen yaƙi marasa matuƙa (drones) a duniya.
Tangarɗa a dangantaka da Amurka
Najeriya na kuma ƙarfafa hulɗa da wasu ƙasashen Afirka, ciki har da Masar, wadda ta nuna aniyar haɗa kai da Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci a Afirka ta Tsakiya da Yamma da yankin Sahel.
Masana sun ce wannan yunƙuri na nuna sauyin salon manufofin ƙetare na Najeriya zuwa tsarin da bai dogara ga ƙasa guda ba.
Kabir Adamu na kamfanin Beacon Consulting ya ce wannan mataki ya dace kuma zai taimaka wajen kare ‘yancin Najeriya tare da rage haɗarin dogaro da tallafin Amurka kaɗai.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa hakan na iya haifar da tangarɗa a dangantaka da Amurka, wadda ta saba kallon irin wannan sauyi a matsayin ƙalubale ga tasirinta.
Wani masani mai fashin baƙi a kamfanin tattara bayanan sirri na SMB Consulting, Confidence MacHarry, ya ce la’akari da yanayin tattalin arziƙin Najeriya, zaɓin faɗaɗa abokan hulɗa shi ne ya fi dacewa maimakon ci gaba da dogaro da neman tallafin tsaro daga Amurka wanda ya bayyana a matsayin mai tsada.
Duk da haka, masana na ganin cewa idan aka tafiyar da lamarin da hikima, zai iya haifar da ingantaccen sakamako a fannin tsaro da zaman lafiya.