Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, tare da haɗin gwiwar maharba, sun samu nasarar tarwatsa gungun masu garkuwa da mutane, tare da kama mutum bakwai da ake zargi da aikata laifuka a Jihohin Gombe, Bauchi, Yobe da Adamawa.

Rundunar ta samu nasarar ne bayan kama Abdullahi Ibrahim, mai shekaru 40 daga ƙauyen Tilde a Funakaye, a ranar 23 ga watan Nuwamba 2025.

An kama shi ne bayan samun bayanan sirri kan hulɗa da masu satar shanu.

Abdullahi, ya amsa cewa yana da hannu a garkuwa da mutane tare da bayyana sunayen waɗanda suke aikata laifin tare.

A cewar kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, jami’an Operation Hattara tare da maharba ne suka kai samame maɓoyarsu a ranar 28 ga watan Nuwamba 2025, inda suka kama mutum shida bayan yin artabu.

Waɗanda aka kama sun haɗa da; Usman Mohammed, Hussain Idris, Adamu Tukur,  Ya’u Abdullahi, Ali Umar, Hassan Usman da Abdullahi Ibrahim.

Rundunar ta ce waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna da hannu a garkuwa da mutane tare karɓar kuɗin fansa kusan Naira miliyan 150.

Jami’an sun shiga dajin Gadam, inda suka samu bindiga ƙirar GPMG mai jigida guda ɗaya da harsasai takwas bayan wata musayar wuta da suka yi wasu ’yan ta’adda da suka tsere.

Haka kuma an gano suna da hannu wajen garkuwa da wani mutum a ƙauyen Barderi a Akko, a ranar 15 ga watan Janairun 2025.

Sun tsare mutumin na tsawon makonni biyu kafin karɓar Naira miliyan 15 a matsayin kuɗin fansa.

DSP Buhari, ya ce ana cigaba da bincike, kuma za a gurfanar da su a kotu.

Ya roƙi jama’a da su ci gaba da bai wa rundunar sahihan bayanai domin inganta harkokin tsaro.

Post masu alaƙa

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano

Babachir Lawal ya fita daga ADC