Daga Ali Rabiu Ali, Dutse
Ma’aikatar Jin-ƙai da Ayyuka na Musamman ta Jihar Jigawa ta dakatar tare da sallamar wasu ‘yan kwangilar ciyar da ɗalibai a makarantun kwana, bisa zargin yin almundahana, ƙara adadin ɗalibai ba daidai ba, da kuma samar da abinci mara inganci.
Matakin ya biyo bayan binciken bazata (sting operation) da ma’aikatar ta gudanar a wasu makarantun kwana da ke ƙaramar hukumar Dutse, a ranar Laraba, 7 ga watan Janairu. Binciken ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ma’aikatar, Honarabul Auwal D. Sankara.
Binciken na da nufin tantance sahihancin shirin ciyar da ɗalibai na jihar, tare da tabbatar da cewa walwalar ɗalibai ba ta zama hanyar samun riba ta kashin kai ba.
A yayin binciken, jami’an sa ido sun gano gagarumar matsala a Makarantar ‘Yan Mata ta Model Boarding School, Kudai, inda aka samu bambanci mai yawa tsakanin adadin ɗaliban da shugabar makarantar ta bayar da rahoto da kuma ainihin adadin da aka kirga.
- Tattaunawa Ce Mafita Ga Rikicin Manoma da Makiyaya a Jigawa-AFAN
- Malaman turanci 337 sun fara samun horon hadin gwiwa a jihar Jigawa
Rahoton ya nuna cewa an bayyana ɗalibai 1,008, amma a ƙididdigar zahiri an samu ɗalibai 681 kacal, wanda ke nuna ƙarin adadi sama da kashi 30 cikin 100.
Haka kuma, miya da aka raba wa ɗaliban an same ta ba ta dace da ci ba, lamarin da ya sa aka dakatar da ɗan kwangila Jibrin Maifata nan take.
A Makarantar Sakandaren Kasuwanci ta Gwamnati, Dutse, jami’an sun ƙi karɓar shinkafa mai rauni da aka kawo wa ɗalibai.
A wani mataki na gaggawa domin tabbatar da doka da oda, Kwamishinan ya sallami Alhaji Sule Zai, wanda ke riƙe da mukamin Shugaban ‘Yan Kwangilar Ciyar da Ɗalibai.
Haka zalika, a Makarantar Larabci da Ilimin Addinin Musulunci, Dutse, an dakatar da ‘yan kwangila uku Kamalu Sulaiman, Alhaji Abdullahi Abanderi da Alhaji Umaru Chamo bayan an same su da kawo kayan abinci ba su cika ka’ida ba.
Sai dai a Makarantar Makafi ta Limawa, an samu abin yabo inda adadin ɗalibai ya dace da ainihin ƙididdigar da aka yi.

Duk da haka, an bar ɗan kwangilar, Adamu Khalid, a kan aikinsa, amma an ja hankalinsa sosai da ya tabbatar da daidaiton samar da abinci, tare da ƙara sinadaran gina jiki kamar furotin da ‘ya’yan itatuwa, kamar yadda ɗaliban makarantar suka nema.
Kwamishinan Ma’aikatar, Hon. Auwal D. Sankara, ya jaddada cewa gwamnatin Jihar Jigawa ba za ta lamunci duk wani nau’i na almundahana ko sakaci a shirin ciyar da ɗalibai ba.

Ya ce gwamnatin Gwamna Umar Namadi Danmodi na ci gaba da aiwatar da ajandar maki 12, musamman wajen kare lafiyar yara da tabbatar da ingantaccen ilimi.
Ya gargadi duk wanda aka samu yana karkatar da dukiyar da aka ware domin ciyarwa da ilimin yara cewa zai fuskanci hukuncin doka, tare da tabbatar da cewa binciken bazata zai ci gaba a fadin jihar.
Matakin da gwamnati ta ɗauka ya samu karɓuwa daga iyaye da masu ruwa da tsaki, inda suka bayyana cewa hakan alama ce ta ƙudirin gwamnati na kare haƙƙin ɗalibai da inganta shirin ciyar da makarantu.

