Babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Farida Rabi’u Danbaffa, ta fara sauraren shaidu kan tuhumar da ake yiwa, Sha’aibu Abdulkadir Chediyar Kuda , da zargin kisan kan wata matar aure mai suna, Ruma Shu’aibu, a ranar 6 ga watan Afrilun 2025.
A zaman kotun na ranar Alhamis lauyan gwamnatin jihar Kano kuma mai gabatar da kara, Barista Basiru Kabiru Aliyu, ya gabatar da shaidu guda biyu, wadanda suka hada da mijin matar mai suna, Ibrahim Muhammad da kuma budurwar wanda ake tuhumar mai suna, Asiya Abdulmalik.
Asiya Abdulmalik ta shaidawa kotun cewa, ta taba bayyana wa saurayin ta wato wanda ake tuhuma cewa, zata je gidan Ruma, don ta duba ta sakamakon aikin da tiyata da aka yi mata, inda wanda ake zargin ya ce zai rakata suje tare.
Shaidar ta ce sunje gidan Rumasa’u dake unguwar Tsamiyar Duhuwa, a karamar hukumar Kumbotso Kano tare da wanda ake tuhumar suka gaisa sannan suka bar gidan.
- Sheikh Dahiru Usman Bauchi Ya Rasu
- Shugaba Tinubu Ya Aike Wa Majalisa Sunayen Mutane 3 Da Za A Nada Jakadun Nijeriya
Sai dai ta kara da cewa, akwai lokacin da marigayiyar ta kirawo ta awaya, har ta roketa ta tura mata Data,inda ta bayyana mata cewe bata da kudin da zata iya tura mata Data, daag bisani sai ta roki saurin ta ya tura Data kuma ta tura masa nambar Ruma’asu, amma daganan bata sani ba ko ya tura mata ko kuma bai tura ba.
Anasa bangaren mijin matar ya shaida wa kotun cewa, ya fita daga gida da karfe 2:00pm na rana, kuma sun sabayin waya da ita amma ya kirawo wayarta bai sameta ba, sai da ya kirawo wata makociyarsu don ta bincika masa, inda ita ma ta kwankwasa gidan tare taji shiru kuma wayarta taki shiga.
Kotun dai ta sanya ranar 22 ga watan Janairu 2026 don ci gaban sauraren shaidun.