Kogi Ta Haramta Bukukuwan Yaye Yara da “Sign-Out” a Makarantu

Gwamnatin Jihar Kogi ta haramta bukukuwan yaye yara a makarantun firamare da sakandire a matsayin wani ɓangare na gyaran tsarin ilimi.

Wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan Ilimi na jihar, Wemi Jones, ya fitar yayin taron masu ruwa da tsaki a Lokoja ranar Laraba, 3 ga Satumba, 2025.

Sanarwar ta ce, an haramta bukukuwan “sign-out” na ɗalibai a makarantun saboda tasirin da hakan ke yi wajen ƙara matsin tattalin arziƙi ga iyaye da haifar da ɗabi’u marasa kyau.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati ta ɗauki matakin ne domin rage wa iyaye nauyin da ke kansu, da kuma samar da hanyoyin da suka fi dacewa wajen murnar kammala karatu ga ɗalibai.

Gwamnatin ta tabbatar da cewa sabbin ƙa’idojin za su fara aiki nan take, tare da kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cikakken bin dokar ilimi da aka kafa tun 2020.

 

Post masu alaƙa

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Yan Sandan a Kano sun kama mutane 244, ciki har da 117 da ake zargi da fadan daba.

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.