Rundunar ’yan sanda a Jihar Kebbi ta cafke wata mai suna Maryam Atiku, mai shekaru 20, bisa zargin binne jaririyar da ta haifa da ranta a unguwar Nasarawa da ke cikin garin Kamba, Karamar Hukumar Dandi.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
A cewarsa, bayan Maryam haihu ne ta nannade jaririyar da zanen atamfa guda uku sannan ta kai ta wani daji mai suna Malam Yaro. A nan ta tono rami ta binne jaririyar da ranta.
- Gwamnatin Kano Za Ta Sake Yi Wa Zawarawa Da Yan Mata Auren Gata
- Tinubu Ya Mayar Da Shugaban NTA Salihu Dembos
Sai dai wani manomi a yankin, Alhaji Kabiru Muhammad, wanda ya je gonarsa da ke kusa da wurin, ya lura da wani sabon wurin da aka tona mai kama da ƙaramin kabari. Wannan ne ya sa ya yi kira da a kawo masa agaji. Mutane suka taru, inda aka tono jaririyar, aka same ta da ranta.
An garzaya da jaririyar Asibitin Gwamnati na Kamba, inda likitoci suka tabbatar da cewa tana cikin ƙoshin lafiya.
Rundunar ’yan sanda ta ce nan take aka kama matashiyar, kuma tana tsare a sashen binciken manyan laifuka (SCID) da ke Birnin Kebbi. Maryam ta amsa laifinta, inda daga bisani aka gurfanar da ita a gaban kotu.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Bello M. Sani, ya yaba wa matar gwamnan Kebbi, Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris, bisa alƙawarin ɗaukar nauyin kula da jaririyar.
Haka kuma, ya jinjinawa Alhaji Kabiru Muhammad, (manomi) bisa rawar da ya taka wajen ceton rayuwar jaririyar.