Gwamnatin Kano Za Ta Sake Yi Wa Zawarawa Da Yan Mata Auren Gata

Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar da auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi.

Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin.

Sheikh Daurawa ya ce a wannan karon angwaye da amaren za su mori gwaggwaban tanadi na musamman daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.

Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban 2023 ne Gwamnatin Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 wanda ta ɗauki watanni tana shiryawa.

Tun bayan hawansa mulki ne, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa zai yi wa matan da ba su da galihu auren gata, ta hanyar samar musu da dukkan kayayyakin da mace ke bukata a gidan aure da kuma yi musu walicci.

A wancan lokacin, ɗaura aurarrakin ne a wasu masallatan Juma’a a dukkan ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar.

A babban Masallacin Juma’a na gidan Sarkin Kano kawai an daura auren kusan mutum 300 wanda shi ne Gwamna Abba Kabir Yusuf da Shugaban Hisbah Sheikh Daurawa, wanda shi ne jagoran hidimar suka halarta.

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya yi walicin angwaye yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zama waliyyin amare a kan sadaki Naira 50,000 ga kowace amarya.

Gwamnan Jigawa Umar Namadi na daga cikin waɗanda suka harlaci daurin auren.

Post masu alaƙa

‘Iran ta buɗe wa wani jirgi wuta a mashigar Hormuz

Ƙungiyoyin PDP 293 sun koma APC a Yobe

Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026 na naira tiriliyan 68