Majalisar Dokokin Jihar Kuros Riba ta dakatar da wasu kansiloli huɗu na Ƙaramar Hukumar Akpabuyo na tsawon wata uku.
Majalisar ta dakatar da su ne bisa zargin aikata ayyuka yadda suke so da kuma nuna rashin biyayya ga dokoki.
Kansilolin da dakatarwar ta shafa su ne, Honarabul Innocent Meukpa da Honarabul Patrick Eyo Elim da Honarabul Bassey Effiom Edem da kuma Honarabul Tete Oyoyo Ubene
Ana zargin kansilolin da yin watsi da ayyukan da ke gabansu tare da nuna halin ko-in-kula ga al’amuran ƙaramar hukumar.
A baya-bayan nan ma, majalisar dokokin Kuros Riba ta dakatar da Honarabul Idi Yakubu, mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Ogoja, bisa zargin watsi da aikinsa da shiga sharholiya, lamarin da ya sa ya yi watsi da duk wasu ayyuka na ƙaramar hukumar.