Kwankwaso ya amince a ba wa Kudu takarar Shugaban Kasa ta NDC

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya goyi bayan matakin jam’iyyar NDC na ba da takarar shugaban kasa ta 2027 ga yankin Kudancin Najeriya.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin Babban Taron Jam’iyyar na Ƙasa da aka gudanar a Abuja ranar Asabar, inda ya ce matakin ya yi daidai da tsarin rabon madafun iko da jam’iyyar ta amince da shi.

“Na goyi bayan ba da takarar shugaban ƙasa ga yankin Kudu domin yankin ya cika wa’adinsa na shekaru takwas.

Ya kuma buƙaci ’yan Najeriya da magoya bayan jam’iyyar da su ci gaba da taka rawa wajen wayar da kai da tattara goyon baya gabanin babban zaben 2027.

Wakilinmu ya ruwaito cewa tun da farko taron jam’iyyar ya amince da ware takarar shugaban kasa ga Kudancin Najeriya na wa’adi daya kacal na shekaru huɗu.

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Ogbaru ta Jihar Anambra, Afam Victor Ogene, ne ya gabatar da ƙudurin, wanda wakilan taron suka amince da shi baki ɗaya.

Taron ya kuma amince cewa bayan wa’adin shekaru huɗun, takarar shugaban kas7a za ta koma yankin Arewa kai tsaye.

Matakin ya buɗe wa tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, da sauran masu neman takara daga yankin Kudancin Najeriya hanya.

A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Cleopas Moses Zuwoghe, ya sake jaddada ƙudirin NDC na kare dimokuraɗiyya, bin tsarin mulki da kuma ci-gaban ƙasa

Post masu alaƙa

Yan sandan Kano sun shirya taron masu duwa da tsaki bayan zanga-zanga a Ungogo

Najeriya ta ƙarfafa ƙawancen tsaronta da Amurka

EFCC ta ayyana neman Sadiya Farouq ruwa a jallo