Yan sandan Kano sun shirya taron masu duwa da tsaki bayan zanga-zanga a Ungogo

Rundunar yan sandan jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Kwamishinanta, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ta shiga tsakani don dawo da zaman lafiya a kauyen Jajira dake karamar hukumar Ungogo, bayan wasu matasan sun gudanar da zanga-zanga da ka iya tayar da hankali.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce bayan faruwar lamarin, kwamishinan yan sandan jihar ya tura tawagar jami’an yan sanda ƙarƙashin jagorancin mukaddashin kwamishinan yan sanda ,DCP Lawal Isah Mani, wanda ya gana da jama’ar yankin  tare da kwantar musu da hankali

Tunda farko al’ummar yankin Jajiran, sun yi zargin an rufe musu hanya saboda aikin layin dogo da ake gudanarwa, inda suka nuna rashin amincewarsu.

Sanarwar ta ce rundunar ta shirya taron masu ruwa da tsaki na karamar hukumar a hedikwatar ‘yan sanda dake Bompai.

Taron ya samu halattar mataimakin shugaban karamar hukumar Ungoggo , Hon. Auwal Idris Isah da Hakimin Ungoggo, Alhaji Nura Shehu Ahmad da Dagacin Jajira Malam Ibrahim Muhammad da wakilin ma’aikatar Sufuri ta Tarayya da akilin kamfanin dake gudanar da aikin da sauran masu ruwa da tsaki daga garin Jajira dama Ungogo.

A yayin taron, an tattauna matsaloli tare lalubo hanyoyin magance matsalar data faru

Kwamishinan ‘Yan Sanda CP Ibrahim Adamu Bakori ya shawarci jama’ar yankin su zauna lafiya, sannan su guji yin abunda zai tayar da hankalin al’umma.

 

Post masu alaƙa

2027: Sarkin Gumel Alhaji Dr. Lawan Ahmad Muhammad Sani, Ya Tabbatar Wa Namadi Da Kuri’un Al’ummar Masarautar

Ba za mu lamunci tada zaune tsaye ba a yayin tarukan siyasa—Tinubu

Tinubu zai ƙaddamar da titin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Kano a watan gobe