• Home  
  • Kwastam Ta Kama Kudin Kasar Waje A Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano.
- Babban Labari - Kasashen Ketare - Labarai

Kwastam Ta Kama Kudin Kasar Waje A Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano.

Hukumar yaki da hana fasa kwauri ta kasa (NCS) shiyar Kano da Jigawa, ta kama wasu kudaden kasashen waje, sama da naira miliyan 600, tare da kama wasu mutane uku da ake zargi a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano (MAKIA). Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron manema labarai tare […]

Hukumar yaki da hana fasa kwauri ta kasa (NCS) shiyar Kano da Jigawa, ta kama wasu kudaden kasashen waje, sama da naira miliyan 600, tare da kama wasu mutane uku da ake zargi a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano (MAKIA).

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron manema labarai tare da hadin gwiwa da Kwanturolan Rundunar Kano/Jigawa, Dalhatu Abubakar, da Daraktan Shiyya na Hukumar EFCC na Kano, Ibrahim Shazali suka yi.

Abubakar ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne da wasu kudaden kasashen waje da aka boye a cikin jakunkuna. Daya daga cikinsu mai suna Ahmed Salisu, wanda yake da fasfo na kasar Ghana mai lamba G5347658 ya isa Najeriya daga kasar Saudiyya a cikin jirgin kasar Habasha da misalin karfe 12:15 na rana. a ranar 7 ga Yuli, 2025.

Ya bayyana cewa jami’an hukumar ne suka kama wadanda ake zargin da kudaden kasashen waje wadanda suka tattara sahihan bayanan sirri tare da hadin gwiwar wasu hukumomi a ciki da wajen kasar.

Ya kara da cewa, da isowar wanda ake zargin kamar sauran fasinjojin, an tuna masa da wajibcinsa na bayyana duk wani kudin waje ko kayan aiki da ya wuce dala 10,000, amma ya ki yin hakan.

Abubakar ya ce , bisa ga bayanan sirri, an tsare wanda ake zargin don ci gaba da bincike, A yayin binciken jami’an sun gano wasu kudade na kasashen waje da aka boye a cikin kwalayen tufafi, da aka kiyasta adadin kudaden da aka kama sun ₦653,987,268.50.

Ya bayyana boyewar a matsayin wani yunkuri na kaucewa ganowa, yana mai jaddada cewa, rundunar zata ci gaba da jajircewa,don kama masu aikata laifukan fasa kwauri.

Ya kuma kara da cewa rundunar tare da hadin gwiwar EFCC sun fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin kafin a gurfanar da su a gaban kotu.

Daraktan shiyya na hukumar EFCC, Ibrahim Shazali, ya yabawa hukumar kwastam ta Najeriya bisa nasarar gudanar da aikin da ya dace.

Da yake magana a madadin Shugaban Hukumar EFCC, Mista Ola Olukoyede, Shazali ya bayyana matukar jin dadin hadin gwiwar da hukumomin biyu ke yi.

Ya ce aikin na hadin gwiwa ya nuna aniyarsu ta tabbatar da tsaron iyakokin Najeriya da yaki da laifukan rusa tattalin arziki

A cewarsa, aikin da aka yi a ranar 7 ga watan Yuli a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma gudanar da bincike mai zurfi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai