Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci Tinubu ya umarci rundunonin sojin ƙasar su ɗauki ƙairin jami’an aƙalla 100,000 domin ƙarfafa yaƙin da gwamnati ke yi da matalar tsaro a ƙasar.
Matakin na zuwa ne bayan da ɗan majalisar dattawa daga jihar Kebbi, Yahaya Abdullahi ya gabatar da ƙudiri kan batun, inda ya alaƙanta hakan da sace ɗalibai 25 na sakandiren yanmata a jihar Kebbi.
Sanata Yahaya ya ce ace ɗaliban cin fuska ne ga hukumomin ƙasar, yana mai cewa sace ɗalibai a makarantu zai hana ɗalibai mata zuwa makarantu a ƙasar.
A nasa ɓangare Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ya nuna damuwarsa kan yadda ake yawan sace ɗalibai a makarantunsu a ƙasar.
Tuni dai majalisar ta kafa kwamiti da zai binciki lamarin da yadda ake tafiyar da kuɗaɗen da aka ware wa shirin kare makarantu na ƙasar

