Jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens sun aika mayaƙan Boko Haram kimanin 50 barzahu yayin musayar wuta a Jihar Kaduna.
Hukumar NSCDC ta bayyana cewa, mayaƙan na Boko Haram sun gamu da ajalinsu ne bayan sun yi wa jami’anta kwanton ɓauna ranar Litinin.
Kakakin Hukumar Sibil Difens, Babawale Afolabi, ya ce jami’an hukumar sun yi arangama da mayaƙan ne a lokacin da suke sintirin kare babban layin wutar lantarki da ya taso daga yankin Shiroro a Jihar Neja.
- Ba Tsoron Gwamnonimu Mu Ke Yi Ba…-Sarkin Musulmi
- Matsayar Malaman Addinin Musulunci A Najeriya Dangane Da Kudurin Haraji
Babawale Afolabi ya ce “Mayaƙan Boko Haram kimanin 200 ɗauke da muggan makamai ne suka kai wa jami’an mu kusan su 80 hari a yankin ƙauyen Farin Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Cikun da ke Jihar Kaduna.
“Daga ganin ayarin motocin jami’an suka buɗe musu wuta, saboda wai ayyukan jami’an tsaron sun takura musu a yankin.
“Amma jami’an namu sun yi nasarar halaka 50 daga cikin maharan, ko da yake ba a ga mutum bakwai daga cikin jami’an namu ba tukuna. Akwai wasu kuma da suka samu raunuka a yayin musayar wutar,” .