NAHCON ta ɗauki mataki bayan mahajjatan Najeriya sun yi bore kan rashin ingancin abinci

Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da ingancin abincin mahajjata yayin aikin Hajjin 2026 da ake gudanarwa.

Wannan dai na zuwa ne bayan da mahajjatan Najeriya suka ƙi cin wani abincin dare da aka tanadar musu ranar Talata a Saudiyya.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, NAHCON ta bayyana cewa hukumomin lafiya na Saudiyya na ci gaba da aiwatar da tsauraran matakan imganta abinci domin tabbatar da jin daɗin dukkan mahajjata, musamman la’akari da yanayin zafi da ake fama da shi a ƙasar.

Sanarwar ta ce wasu daga cikin abincin dare da aka bayar a ranar 27 ga Mayun 2026 ba su cika ƙa’idojin da suka shafi sarrafawa da mazubinsa ba, saboda haka aka yi watsi da su nan take tare da haɗin gwiwar jami’an NAHCON.

Domin rage wa mahajjatan da abin ya shafa raɗaɗi, kamfanin da ke kula da hidimar abinci ya samar da wasu kayan ƙwalam na wucin gadi, yayin da mambobin hukumar NAHCON suka zagaya domin yi wa jami’an jihohi bayani tare da kwantar musu da hankali.

Shugaban hukumar NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya umarci kwamitin tsaro na hukumar da ya gudanar da bincike kan masu samar da abincin da kuma waɗanda suka taimaka wajen ba su kwangilar.

Haka kuma ya ba da umarnin gudanar da bincike kan wasu masu shirya tafiye-tafiyen Hajji da ake zargi da shigo da Alhazai fiye da adadin da suka yi rajista da kuma amfani da Alhazai ta hanyar da ba ta dace ba.

Hukumar ta ce duk wanda aka samu da laifi bayan bincike zai fuskanci hukunci, har da soke lasisin aiki.

NAHCON ta kuma tabbatar da cewa an fara shirye-shiryen mayar wa Alhazan da lamarin ya shafa kuɗaɗensu.

Post masu alaƙa

Mun shimfiɗa tubalin magance matsalolin Najeriya – Tinubu

Aminu Abdussalam ne ɗantakararmu na gwamna a 2027 – Kwankwaso

Tsadar kayan abinci ta jefa mu cikin tsaka mai wuya — Mazauna Abuja