Najeriya za ta fara ƙera motocin yaƙi da na’urorin daƙile daƙike ‘drone’

Najeriya na ƙara ƙaimi wajen bunƙasa samar da kayan aikin soji a cikin gida, yayin da Kamfanin Masana’antun Tsaro na Najeriya (DICON-D7G) ke shirin fara ƙera motocin yaƙi masu sulke, na’urorin daƙile jirage marasa matuƙa da sauran kayan aikin tsaro na musamman.

Ana aiwatar da shirin ne tare da haɗin gwiwar kamfanin Eagles International for Defence Systems, kuma ana sa ran hakan zai taimaka wajen musayar fasahar zamani, samar da ayyukan yi da kuma rage dogaro da shigo da kayan aikin soji daga ƙasashen waje.

Babban Daraktan DICON-D7G, Mista Osman Chennar, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, bayan ziyarar duba masana’antu da wuraren ƙera kayan aikin soji da tawagar Ministan Tsaro, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya kai birnin Alƙahira na ƙasar Masar na tsawon kwanaki biyu.

Chennar ya ce haɗin gwiwar zai samar da guraben ayyukan yi ga sama da ma’aikata 200, tare da ba da damar aiki ga kusan tsofaffin jami’an soji 100 da suka yi ritaya.

Ya ce yarjejeniyar za ta kuma samar da ɓangarorin ƙera kayayyaki da za su ba Najeriya damar samun fasahohin soji na zamani ta hanyar musayar ilimi da ƙwarewa.

A cewarsa, shirin zai bai wa Najeriya damar ƙera nau’o’in aikin soji da dama domin amfani ga rundunonin sojinta, tare da yiwuwar sayar da wasu daga cikinsu ga sauran ƙasashen Afirka.

Daga cikin motocin da ake shirin samarwa akwai Armoured Multi-Purpose Vehicle BR6, gidan ɗaukar dakaru mai sulke, gidan harba rokoki na mortar mai girman 120mm da kuma motocin ɗaukar marasa lafiya da na fitar da waɗanda suka samu raunuka daga wuraren yaƙi.

Sauran kayan aikin sun haɗa da motocin yaƙi masu sulke na MRAP-Buffalo U.10 da M.12, MRAP-Buffalo F-4, motar Rhino Guard GXR mai kariya daga jirage marasa matuƙa da rokoki na RPG, APC Moon PT6, motar GXR Phantom mai sauƙin nauyi da kuma BMP-2 Infantry Fighting Vehicle.

Post masu alaƙa

Ambaliya ta mamaye wasu sassan Abuja

Sojojin sun kashe ‘ƴan ta’adda’ tare da ƙwace abubuwan fashewa 180 a Zamfara

INEC ta kai wa CBN ajiyar muhimman kayan zaɓen Gwamnan Osun