NOA Ta Bukaci Dalibai Su Ci Gaba Da Martaba Nijeriya Da Al’adunsu.

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta bukaci yara da dalibai su kasance masu nuna kishin kasar su da bin doka don zama wadanda za a yi alfahari da su anan gaba.

Darakta Janar, na jukumar NOA Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi baƙuncin ɗaliban makarantun, CK Academy, Bmuko Dutse, da kuma Goldsworth Resource Development Academy, a zaman tattaunawa da gudanar a hedikwatar hukumar dake birnin tarayya Abuja.

Ya gabatar wa yaran da Dokoki Bakwai na Ɗan Ƙasa Nagari, tare da bayyana muhimmancin bin su domin gina Najeriya ta gari.

Ya kara da cewa hukumarNOA, za ta ci gaba da wayar da kan jama’a ta hanyar shirye-shieyen da gwamnati ta ke shiryawa don samun hadin kan kasa

A nata jawabin, Mrs Cynthia Opene shirin Kiddies World NTA Channel 5, ta yaba da tarbar da NOA ta yi, tana mai cewa ziyarar ta nuna irin rawar da hukumar ke takawa wajen tarbiyyar yara.

A karshe Mallam Lanre Issa-Onilu ya yara sune manyan gobe don haka su zamo masu nuna kyakkyawar halayya a duk inda suka samu kansu don a yi alfahari dasu anan gaba.

Post masu alaƙa

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano

Babachir Lawal ya fita daga ADC

DSS ta kama mutane 5 da ake zargi da sace ɗaliban makarantar St. Mary’s Pipiri a jihar Neja