NUJ Ta Ziyarci Tashar MUHASA

Exif_JPEG_420

A yau Juma’a 18 ga watan Oktoba ƙungiyar yan jarida ta ƙasa reshen jihar Kano ƙarkashin jagorancin Sulaiman Abdullahi Dedere ta kawo ziyara gidan rediyo da talabijin na muhasa domin karfafa alaƙar dake tsakanin su.

Shugaban ƙungiyar ya bayynana farin cikinsu su, da kuma maƙasudin kawo ziyarar.

Dedere ya kuma yi kira ga yan jarida musamman na jihar kano da su hanzarta yin rajista da kungiyar.

Shugaban ya bayyana cewa zuwa yanzu gidajen jarida 11 ne kawai ke da Rajista da kungiyar a nan Kano.

A na ta bangaren shugabar gidan rediyo da talabijin na MUHASA Hajiya Aishatu Sule ta bayyana farin cikinta da wannan ziyara.

Taron ya samu halartar sakatariyar ƙungiyar ta ‘yan jarida da sauran jami’ai.

Daga ɓangaren ma’aikatan Muhasa Hajiya Amina Yahaya Deen da Abdullahi Musa Huguma da Ummi Muhammad Kuchazi na daga cikin waɗan da suka samu halartar zaman.

Post masu alaƙa

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta bayyana Muhasa TVR a matsayin kan gaba wajen gyaran tarbiyyar al’umma.

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda