Rundunar ƴan sandan Kano ta ƙwato baburan Adaidaita sahu na sata guda 8 da kama waɗanda ake zargi.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta samu nasarar kama mutane uku da ake zargi da satar baburan adaidaita sahu, tare da kwato guda 8 da aka sace daga jihar.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar CSP, Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Sanarwar ta ce a ranar 26 ga watan Maris 2026,  jami’an ƴan sanda dake aiki a ofishin ƴan sanda na Kwakwachi, lokacin da suke aikin sintiri akan titin Airport Road, ne suka tare wani matuƙin adaidaita sahu mai suna Abubakar Sidi Kaduna, amma ya gaza yin bayani kan baburin adaidaia sahun , inda aka mika shi sashin binciken laifuka.

Binciken ƴan sandan ya gano cewa wanda ake zargin ya haɗa kai da wasu mutane biyu da yake kaiwa baburan idan ya sata , da suka haɗa da Abba Ɓaɓura da Babangida Haruna dukkansu mazauna Ɓaɓura a jihar Jigawa.

Rundunar ƴan sanda ta yi kira ga al’umma, musamman matuƙa baburan adaidaita sahu, su gujewa karɓar abin sha ko kyauta daga mutanen da ba su sani ba.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da ƙoƙarin jami’an da suka gudanar da wannan aiki, tare da jaddada aniyar rundunar na ci gaba da yaƙi da masu yunƙurin aikata laifuka.

 

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda