Rundunar ƴan sandan Kano tare haɗin gwiwar sojoji sun ƙwato Shanu 67 daga hannun ɓarayi

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, tare da haɗin gwiwar sojoji sun yi nasarar ƙwato shanu 67 da Jaki ɗaya da Tunkiya ɗaya daga hannun masu satar Shanu a ƙaramar hukumar Gwarzo.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Sanarwar ta bayyana cewa, sun ɓarayin shanun sun sace dabbobin daga wasu ƙauyukan Gwarzo, inda jami’an tsaron suka garzaya wajen da lamarin ya faru tare da yin musayar wuta da ɓarayin har jami’an suka yi nasara akansu lamarin da ya tilasta mu su barin dabbobin suka tsere.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa da ƙoƙarin da jami’an tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da yaƙi da masu yunƙurin aikata laifuka a faɗin jihar.

Rundunar ƴan sandan ta ce tuni an mayar da dabbobin ga masu su bayan tantancewa.

Post masu alaƙa

Tinubu ya tura Shettima ya wakilci Najeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Amurka

APC ta ƙalubalanci Atiku ya yi bayani dalla-dalla kan yadda zai dawo da tallafin mai

NAHCON ta musanta zargin karkatar da kujerun Hajjin 2027