Jam’iyyar NDC na gudanar da babban taronta na ƙasa

Jam’iyyar hamayyar ta NDC a Najeriya na gudanar da babban taronta na ƙasa domin zaɓen sabbin shugabanninta.

Matakin na zuwa ne mako guda bayan da manyan jiga-jigan siyasar ƙasar biyu, Peter Obi da Kwankwaso suka sanar da komawa cikinta.

Ɗaruruwan magoya bayan jam’iyyar ne suka taru a harabar wurin gudanar da taron a Abuja.

Akwai bayanai masu ƙarfi da ake yaɗawa cewa Peter Obi da Kwankwaso ne jam’iyyar za ta bai wa takarar shugaban ƙasar a jam’iyyar.

Post masu alaƙa

Tinubu ya tura Shettima ya wakilci Najeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Amurka

APC ta ƙalubalanci Atiku ya yi bayani dalla-dalla kan yadda zai dawo da tallafin mai

NAHCON ta musanta zargin karkatar da kujerun Hajjin 2027