Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta shirya gudanar aiyukan hulɗa da jama’a don ƙarfafa danganta mai ƙarfi tsakanin jami’an tsaro da al’umma, a wani bangare na bikin ranar ƴan sandan Nijeriya ta shekarar 2026.
CP Bakori ya bayyna hakan ne yayin ganawarsa da gidan Talabijin da Radio na MUHASA , inda ya ce bikin na bana, an yi masa take da muhimmancin haɗin kai tsakanin jami’an ƴan sanda da al’umma domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce bisa umarnin babban sufeton ƴan sandan Nijeriya, Olatunji Rilwan Disu, za su gudanar da aiyukan tsaftar muhalli a ƙaramar hukumar Fagge da hulɗa da jama’a da bayar da agajin lafiya a Unguwar Dakata daga ranar 30 ga watan maris zuwa 7 ga watan frilun 2026.
Haka zalika za a motsa jiki ( Walkathon) akan titin Abdullahi Wase daga Mandawari zuwa Tal’udu Flyover da ziyartar babbar kotun tarayya dake Kano da tattaunawa da ƙungiyoyin farar hula don ƙara fahimtar juna da haɗin kai.
CP Bakori ya ƙara da cewa za a tattauna da ɗaliban jami’ar North-West da wasan ƙwallon ƙafa a filin wasa na Sani Abacha, Kofar Mata da ziyartar tashoshin motoci da kasuwanni don ilimantar da al’umma a faɗin jihar.
Kwamishinan ƴan sandan ya ce, shirye-shiryen za su samu halartar ƙungiyar matan ƴan sanda, POWA da kwamitin hulɗa tsakanin ƴan sanda da al’umma PCRC da ƙungiyoyin farar hula.
babban bikin ranar ƴan sandan za a kammala shi a ranar 7 ga watan Afrilun 2026, a filin taro na Eagle Square, a birnin tarayya Abuja, inda babban sufetn ƴan sandan Nijeriya, Olatunji Rilwan Disu, zai jagoranci manyan baƙi da masu ruwa da tsaki don gudanar da bikin.
Rundunar ta ce waɗannan aiyukan na cikin ƙudirinsu na nuna haɗin kai da al’umma, domin ƴan sanda a shirye suke wajen ci gaba da aiki da al’umma don magance matsalar tsaro a jihar Kano.
A ƙarshe ya godewa al’ummar jihar Kano, bisa goyon bayan da suke bayarwa don tabbatar da tsaro a faɗin jihar.