Rundunar ‘Yan Sanda Sun Raba Wa Iyalai da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu Naira miliyan 23,574,204

Kwamishinan ‘yansandan Jihar Zamfara, Muhammad Bunu, a madadin babban sufeton ‘yansanda na kasa, Usman Alkali Baba ya gabatar da check ɗin kudi na Naira miliyan 23,574,204 ga iyalai da ‘yan uwa 21 na jami’an ‘yansanda da suka rasa rayukansu a bakin aiki.

Kakakin ‘yansandan Jihar, ASP Yazid Abubakar, ya bayyana haka a takardar da ya sa wa hannu ga manema labarai a Gusau.

A cewarsa, Kwamishina Bunu, a lokacin da yake gabatar da check ɗin kudin, ya yaba wa Sufeton ‘yansandan bisa irin wannan karimcin da ya nuna, sannan kuma ya bukaci iyalan jami’an da suka mutu da su yi amfani da kudaden wajen kula da iyalansu cikin adalci.

Abdulrahman Ahmed, daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin a jawabinsa a madadin sauran wadanda suka amfana, ya mika godiyarsa ga Sufeto Janar na ‘yansanda da kuma rundunar ‘yansanda bisa tallafin da suka ba su, ya kuma ba da tabbacin cewa za a kashe kudaden da aka ba su ta hanyar da ta dace.

Post masu alaƙa

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro