Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar Kano ta Sanya dokar takaita zurga-zurga a kananan hukumomin Ghari da Tsanyawa da kuma Bagwai da shanono, inda za a gudanar da zaben cike gurbi a ranar asabar mai zuwa .
Dokar za ta Fara aiki daga 12 na daren Ranar juma’a har zuwa karfe 06 na yammacin Ranar Asabar 16 ga watan Augusta, 2025, an haramtawa kowa yawo da makami ko wata alamar jam’iyya a ranar zaben”.
Sanarwar ta ce Rundunar zata hada Kai da dukkanin hukumomin tsaro dake jihar Kano don tabbatar da an yi zaben cikin lumana.
Haka zalika kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa,ya ce rundunar ta haramtawa jami’an KAROTA da yan vigilante da Shiga cikin aikin Samar da tsaro a kananan hukumomin da za a gudanar da zaben.
Idan ba a manta ba rundunar ta Yi Wani zama na musamman da shugabannin jam’iyu da kuma masu ruwa da tsaki , wadanda suka rattaba Hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.
Koda a ranar laraba sai gamayyar hukumar tsaron jihar suka gudanar da Wani kan yadda za su tabbatar an gudanar da zaben lafiya ba tare da tashin hankali ba .