Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi ƙarin bayani kan wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna jami’an wasu ƴan sanda biyar sanye da kayan sarki suna taimaka wa wani ɗan siyasa wajen shirya jama’a domin karɓar kuɗi.
Wata sanarwa da ta fitio daga ofishin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce, bayan gudanar da cikakken bincike, rundunar ta tabbatar da aukuwar lamarin bayan wani biki da aka gudanar a ɗakin taro na Coronation dake fadar gwamnatin jihar Kano a ranar Alhamis 10 ga watan Yuli, 2025, wanda bai da alaƙa da zabukan cike gurbi da aka gudanar a ranar 16 ga watan Agustan 2025.
Sanarwar ta ƙara da cewa binciken ya nuna cewa an tura jami’an wajen taron ne domin su tabbatar da tsaro, amma daga bisani bidiyonsu ya bayyana inda suke aikata abin da rundunar bayyana a matsayin rashin ɗa’a.
Rundunar ƴan sandan ta tabbatar wa da cewa ana ɗaukar matakan ladabtar da jami’an domin kiyaye mutunci da ƙwarewar rundunar ƴan sandan Najeriya.