Sarkin Kano Na 14 Muhammadu Sunusi ii Ya Bayyana Takaicinsa Kan Fadan Daba Da Shan Kayan Maye

Mai Martaba Sarkin Kano na 14m Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya bayyana takaicinsa yadda ake fama da fadan daba da shan miyagun kwayoyi da  sace-sacen wayoyin da suka zama ruwan dare a jihar nan.

Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da yake samun korafe-korafen al’ummar  a unguwannin Sheka da Maidile da Ja’oji da dai sauran wasu unguwannin dake cikin birni Kano.

 

Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya ce abun takaici shi ne yadda za ka ga yawancin masu fadan daban matasa ne Yan shekara ashirin da ɗoriya, waɗanda suke ardabar mutane a Yankunansu.

Daya daga cikin Wakilin al’ummar unguwannin sun shaida wa sarkin cewa yawancin fadan daban Yana samo asali ne tun daga  gidan adana namun daji wato Gidan Zoo inda ake yin wasannin na gala da sauransu.

 

Wakilinmu na masarauta Kano  Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa bayan kammala karbar korafen-korafen al’ummar ne sarkin ya shawarci shugabannin kananan hukumomi da hakimai da masu unguwannin da dagatai da limamai da a hada Kai da jami’an tsaro wajen ganin  an kawo karshen fadan daban da shan miyagun kwayoyi a jihar nan.

 

 

Post masu alaƙa

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda

‘Talauci ya faɗo daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto