Sarkin Rano Ambasada Muhammad Isah Umar ya yaba da ƙoƙarin ƴan sandan Kano wajen daƙile laifuka.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya kammala rangadin makwanni uku da ya kai dukkan shiyoyin ƴan sanda 11 na jihar, inda ya ƙarƙare da ziyara Rano Area Command.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori , ya yaba da ƙoƙarin dakarun wajen yaƙi da laifuffuka, tare da umartar su,  su ci gaba da gudanar da aikinsu bisa doka kuma su mutunta haƙƙin ɗan Adam, sannan su guji tsare mutane ba bisa ƙa’ida ba da kaucewa cin hanci da rashawa, da duk wani nau’in rashin ɗa’a.

Haka kuma ya buƙace su su kasance masu amsa kiran gaggawa da ƙara sintiri da kiyaye dokokin rundunar

Musamman wajen yin amfani da kafafen sada zumunta.

Bayan haka, Kwamishinan ya kai ziyarar girmamawa ga mai martaba sarkin Rano, Ambasada Dakta Muhammad Isah Umar, inda ya gode masa bisa goyon bayan da masarautar ke bai wa hukumomin tsaro tare da neman ci gaba da haɗin kai wajen tabbatar da zaman lafiya.

A nasa jawabin, sarkin Rano ya yaba da jagorancin CP Bakori, tare da tabbatar masa da cewa masarautar za ta ci gaba da basu cikakken goyon baya a kowanne lokaci.

Haka zalika mai martaba sarkin Rano, ya yaba da matakan da kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ɗauka wajen daƙile faɗan fada da ƙwacen waya a faɗin jihar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, ya ce rangadin ya bashi damar tattaunawa kai tsaye da jami’an tare da ƙarfafa manufar rundunar wajen nuna ƙwarewa da bin doka da mutunta haƙƙin ɗan Adam da kuma ƙara ƙulla kyakkyawar alaƙa da al’umma.

Post masu alaƙa

Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ne ke haddasa matsalolin tsaro a Sokoto – Aliyu

Gwamnatin Tinubu Za Ta Yi Bitar Albashi Mafi Ƙaranci Na N70,000 — Gbajabiamila

Gwamnatin Oyo ta saka dokar hana fita a ƙananan hukumomi 10