Home » Sauya Sheƙa Bayan Cin Moriyar Jam’iyya Butulci Ne — Kwankwaso

Sauya Sheƙa Bayan Cin Moriyar Jam’iyya Butulci Ne — Kwankwaso

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya soki ’yan siyasar da ke sauya sheƙa daga jam’iyyar da a ƙarƙashinta suka samu nasarar lashe zaɓe zuwa wata.

Kwankwaso ya bayyana lamarin a matsayin cin moriyar ganga, yana mai cewa hakan babban kuskure ne a siyasance.

Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne a gidansa da ke Miller Road a Kano yayin da yake karɓar wasu ’yan siyasar da suka sauya sheƙa zuwa NNPP daga Ƙaramar Hukumar Takai.

Kwankwaso ya ƙara jaddada irin juriya da haɗin kai da ke tafiyar Kwankwasiyya duk kuwa da cewa an ta ƙoƙarin ganin an kawar da hankalin mabiya.

“Duk mun ga abin da ya riƙa faruwa a tarihi, musamman a shekarar 2015 lokacin da wasu ’yan siyasa suka dawo cikinmu amma ashe mayaudara ne masu mugun nufi a zuciyarsu.

“Waɗannan ’yan siyasa sun yi ƙoƙarin kawo hargitsi a cikin jam’iyyarmu amma ba su yi nasara ba.

“Haka ma lokacin da zaɓen 2019 ya zo duk kowa ya san abin da ya faru. Amma abin da yake faruwa a bayan nan ya koya mana darasi sosai.

“Wannan tafiyar tamu ta Kwankwasiyya tana tare da talakawa a kodayaushe, saboda haka duk wani mai kwaɗayi ba zai iya zama a cikinta ba.

Furucin Kwankwaso na zuwa ne yayin da bayan nan wasu jiga-jigan siyasa a NNPP da tafiyar Kwankwasiyya suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC — ciki har da Sanata Kawu Sumaila da Kabiru Alhassan Rurum da sauransu.

Kodayake a baya-bayan nan shi ma dai Kwankwason ana raɗe-raɗin cewa zai koma jam’iyya mai mulki ta APC.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?