Sheik Bala Lau Ya Kai Ziyara Fadar Sarkin Hadejia

Daga: Muhammad Inuwa Ibrahim

Shugaban kungiyar JIBWIS na kasa, Sheik Dr. Abdullahi Bala Lau, ya ziyarci fadar mai martaba sarkin Hadejia, Dr. Abubakar Adamu Maje CON, a jiya juma’a.

Wannan ne karo na uku da kungiyar Izila ta kasa takai irin wannan ziyarar fadar sarkin Hadejia don yin da’awa sakamakon kawo babbar jami’ar musulinci ta duniya Assalam Global University dake Hadejia a jihar Jigawa.

Cikin wadanda suka yiwa, Bala Lau, rakiya sun hada da skaataren kungiyar, Sheik Muhammed Kabiru Haruna Gombe da kuma sauran manyan malamai dake fadin Nijeriya.

A wajabinsa Shiek Abdullahi Bala Lau, yayi fatan jami’ar zata kawo sauye-sauye masu yawa ga al’ummar musulmin duniya baki daya.

Mai martaba sarkin Hadejia, Dr. Abubakar Adamu Maje CON,ya godewa musu bisa wannan ziyara da suka kai masa har fadarsa.

Post masu alaƙa

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 26 a Borno

Tinubu ya tafi hutun mako uku

Gwamnatin Kwara ta haɗa mutum 146 da aka sace a Woro da iyalansu