Sheik Pantami ya zargi wasu jami’an gwamnatin Gombe da shirya masa mairci

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, kuma ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ya zargi wasu jami’an gwamnati da bai bayyana sunayensu ba da shirya masa makirci tare da tsoratar da magoya bayansa yayin da yake ci gaba da rangadin godiya a wasu sassan Jihar Gombe.
Pantami ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, kwana guda bayan ziyararsa zuwa ƙananan hukumomin Shongom, Kaltungo da Billiri.
Ya ce manufar ziyarar ita ce ganawa da shugabannin jam’iyyar PDP da kuma magoya bayansa domin gode musu bisa goyon bayan da suka nuna masa.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da harkokin siyasa suka fara ɗaukar zafi a Jihar Gombe gabanin babban zaɓen shekarar 2027, yayin da ‘yan siyasa ke ci gaba da gudanar da rangadi, tattaunawa da ganawa da al’umma domin ƙarfafa dangantaka da magoya bayansu.
Sai dai Pantami ya yi iƙirarin cewa irin tarbar da ya samu a rangadin nasa ta tayar da hankalin wasu mutane, yana mai zargin cewa wani mutum da bai ambaci sunansa ba na ƙoƙarin bibiyar rayuwarsa tare da shirya masa makirci.

Post masu alaƙa

Babandede Ya Taya Shettima Murnar Sake Samun Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

Majalisar Dattawan Najeriya na so a daina yi wa tubabbun Boko Haram afuwa

ADC Ta Rusa Shugabancin Jam’iyyar a Kano, Ta Kafa Kwamitin Riƙo.