Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bar Abuja Talata da daddare zuwa birnin Havana a ƙasar Cuba domin halartar taron ƙolin ƙasashe masu tasowa na G77 gami da ƙasar China.
Mataimakin shugaban ƙasar ya samu rakiyar Ministan Noma da Raya Karkara Abubakar Kyari, da Ministan Kimiyya da Fasaha da Ƙirƙire-ƙir Uche Nnaji da Babban Sakataren Ma’aikatar, da kuma Ministan Harkokin Waje Ambasada Adamu Lamuwa.
A wata sanarwar da Daraktan yaɗa labarai a ofishin mataimakin shugaban ƙasa Olusola Abiola ya fitar ranar Talata, ya bayyana cewa a wajen taron ƙolin na kwanaki biyu da za a fara daga ranar Juma’a 15 ga watan nan na Satumba zuwa ranar Lahadi 17 ga wata, Shettima zai haɗu da manyan shugabannin ƙasashen duniya, a ciki har da babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Gutteres.
Yace taron ƙolin zai duba matakan rigakafin da za a iya ɗauka don magance matsalolin da ke yin tarnaƙi ga cigaban ƙasashen ƙungiyar tare kuma da yin amfani da kimiyya da fasaha da sabbin ƙirƙire-ƙirƙire wajen haɓaka ci gaban al’umma da bunƙasa tattalin arziki.
Abiola ya ƙara da cewa a bayan fagen taron ƙolin, Shettima zai gana da shugabannin wasu ƙasashe da nufin ƙarfafa kasuwancin Najeriya da ƙulla hulɗar zuba jari bisa tsarin gwamnatin shugaba Tinubu na diflomasiyyar bunƙasa tattalin arziki.
Daraktan yaɗa labarai a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa Olusola Abiola yace shugaban ƙasar Cuba Miguel Diaz-Canel kuma shugaban ƙungiyar G77 gami da ƙasar China, shi ne mai masaukin baƙi a taron ƙolin na Havana mai taken matsalolin cigaban da ake fuskanta tare da duba irin rawar da kimiyya da fasaha da kuma ƙirƙire-ƙirƙire za su iya takawa.
Najeriya na cikin ƙasashe 77 masu tasowa da suka kafa ƙungiyar G77 a shekarar 1964.
Ƙungiyar mai ƙawance da wasu ƙasashe 134 masu tasowa, waɗanda ke da kashi 80 cikin ɗari na yawan al’ummar duniya, tana so ne ta ƙarfafa muradun tattalin arzikinsu ta kuma samar da wani ƙwaƙƙwaran matsayin tattauna matsalolin ƙasashen a Majalisar Dinkin Duniya, kamar yadda Daraktan yaɗa labarai a ofishin mataimakin shugaban ƙasa Olusola Abiola ya bayyana a cikin samnarwar da ya fitar.