Shugaba Tinubu Da Shettima Za Su Kashe Miliyan 9000 A Tafiye-tafiyen 2025

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Ibrahim Shettima za su kashe Naira Miliyan dubu tara da ɗari uku da sittin (9,360) a kayan maƙulashe da tafiye-tafiyen cikin gida da waje a baɗi. 

Wannan na ƙunshe ne cikin kundin kudirin kasafin kudi na shekarar 2025 da ya miƙa wa majalisa a ranar Laraba.

Idan ba a manta ba a ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2025 na Naira tiriliyan 49.7 ga majalisar dokoki da ta Dattawan Najeriya.

A yadda aka tsara kasafin kuɗin baɗj, shugaba Tinubu zai kashe Naira miliyan dubu bakwai da ɗari huɗu da arba’in (7,440) wurin tafiye-tafiye da kayan maƙulashe; yayin da mataimakinsa Kashim Ibrahim Shettima zai kashe Naira miliyan dubu ɗaya da ɗari tara (1,900).

Shugaban kasa zai kashe Naira biliyan 6.14 a tafiye-tafiyen ƙasashen waje; yayinda tafiye-tafiyensa na gida za su laƙume Naira miliyan 873.9.

Haka zalika an ware Naira miliyan 431.6 don ciye-ciyen maƙulashen shugaba Tinubu a 2025 idan Allah ya kai mu.

Post masu alaƙa

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 6 a Adamawa