Shugaban jam’iyya mai mulki a jihar Kano NNPP Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce har yanzu basu dawo da tsohon sakataren gwamnatin jiha Dokta Abdullahi Baffa Bichi da Kwamishinan sufuri Muhammad Diggol jam’iyyar su ba.
Dungurawa ya bayyanawa wakilin jaridar daily trust cewa “har yanzu tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dokta Abdullahi Baffa Bichi da Kwamishinan sufurin jihar Kano ba ‘yan jam’iyyar NNPP bane, bincike ne zai bamu alƙibilar abin da ya kamata mu yi”
A kwanakin baya ne dai jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da tsohon sakataren gwamnatin jihar da Kwamishinan sufuri a wani zargi da ta yi na cewa suna nuna rashin ɗa’a kuma suna amfani da ofishin su ba bisa ƙa’ida ba.
- Shugaba Tinubu Da Shettima Za Su Kashe Miliyan 9000 A Tafiye-tafiyen 2025
- Ɗangote Ya Rage Farashin Man Fetur Saboda Bukukuwan Ƙarshen Shekara
Dungurawa ya ƙara da cewa “Bamu da hannu cikin duk wani abu da ke faruwa da su ko ya faru da su a cikin harkokin gwamnati”
Duk da cewa gwamnatin ta ƙyanƙyasa dakatar da sakataren nata ne bisa dalillai na rashin lafiya, jama’a da dama na cigaba da alaƙanta matakin da wata guguwa da ta taso ta neman gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsaya daƙafarsa.