Shugaba Tinubu ya sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2027

Shugaban Najeriya mai ci a yanzu Bola Ahmed Tinubu ya bayyana sha’awarsa ta sake yin takarar shugabancin ƙasar a babban zaɓen 2027, bayan da ya sayi fom ɗin shiga takara a yau Talata.

Ɗan majalisa mai wakiltar Ikeja a majalisar Tarayya, kuma wanda ke jagorantar ƙungiyoyi da ke goyon bayan Tinubu, James Faleke ne ya sayi fom ɗin a madadinsa a Abuja, kan naira miliyan 100.

Sakataren tsare-tsare na jamiyyar APC, Suleiman Argungu ne ya miƙa fom ɗin bayan da aka ƙaddamar da soma sayar da fom ɗin neman yin takara ga dukkanin masu son tsayawa takara.

Post masu alaƙa

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Bamanga Tukur

Majalisar Najeriya ta dakatar da zuwa Afirka ta Kudu

An Kama Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi 7 A Jigawa