Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Zai Halarci Taron Kungiyar ECOWAS Karo Na 63

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai tafi kasar Guinea-Bissau domin halartar taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 63.

Shugaban dai zai samu rakiyar wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun sa, Dele Alake ta bayyana.

Taron da za a za a fara a gobe Lahadi, ana sa ran za a tattauna batutuwan da suka shafi yankin yammacin Afrika, musammanma rahoton zaman taro na 50 na kwamitin samar da zaman lafiya na kungiyar wanda ya kunshi kalubalen tsaro da kasashe mambobin kungiyar ke fuskanta.

Bayan nan akwai rahoton zaman taro na 90 na majalisar ministocin kungiyar ta ECOWAS kan harkokin kudi da aiwatar da kawusanci na bai daya a nahiyar Afirka da kuma rahoto kan halin da ake ciki a Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.

Sauran abubuwan da ake saran tattaunawa a yayin taron, sun hada da shirin ECOWAS na samar da kudin bai daya da da dai sauran su.

Post masu alaƙa

Dalibai huɗu za su wakilci Najeriya a gasar Spelling Bee ta Duniya a China

Babandede Ya Taya Shettima Murnar Sake Samun Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

Ban taɓa haɗuwa da Adeyemi ba — Gbajabiamila