Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce ta halaka sama da ƴan ta’adda 80, a wani ƙauyen jihar Katsina.
Ta ce ta yi nasarar ƙone baburansu 45 sakamakon luguden wutar da ta yi musu a daren ranar Asabar ɗin da ta gabata.
Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da rundunar sojin sama ta Najeriya ta fitar a ranar Litinin.
Sanarwar da daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarun rundunar sojin, Edward Gabkwet ya sanyawa hannu, ta ce an kai harin ne a wata maɓoyar ƴan bindigar da ke ƙauyen Gidan Kare a ƙaramar hukumar Faskari.
Sanarwa sojojin ta ce ta kai harin ne a daren ranar Asabar a lokacin da ta samu rahoton cewa ƴan ta’adda kimanin 100 sun kai hari a wani ƙauyen da ke da nisan kilomita biyar daga Gidan Kare, inda suka ƙone gidajen jama’a.