Sojoji Sun Hana Wike Shiga Wani Fili A Abuja

Wasu jami’an soji da aka jibge don kula da wani fili, sun hana ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, shiga wani fili da ake takaddama akansa.

Wani faifen bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna yadda ministan ya yi, musayar yawu da wani Soja, ta hanyar fadawa juna munanan kalamai da zagin juna.

Ministan yaje wajen da tawagar hukumar kula da gine-gine ta birnin tarayya Abuja.

Tunda farko dai Nyesom Wike, ya so shiga cikin filin amma sojojin suka hana shi, bisa hujjar da suka bayar ta cewa umarnin aka basu daga sama, na hana shiga wajen, inda shi kuma Ministan yaki amincewa da hakan har sai da suka yi musayar yawu da sojojin.

Lamarin ya fusata ministan, wanda ya dinga fadar maganganu marasa dadi ga sojojin, harma yake tambayarsu dalilin da yasa aka hana shi shiga filin.

Sai dai ministan ya ce an hana shi, shiga ne saboda wajen yana da alaka da tsohon shugaban hafsan rundunar sojin ruwa.

Jami’in soja ya bayyana wa ministan cewa an mallaki filin bisa doka da oda, sai dai duk ƙoƙarin jami’an tsaron da ke tare da Wike na ganin an sasanta lamarin, sojojin suka ƙi janye, suna cewa suna bin umarnin daga sama.

Haka zalika Wike ya ce ba zai lamunci irin wannan halin na rashin bin doka ba.

Ministan ya ƙara da cewa tsohon hafsan soja ya kamata ya nemi ofishinsa don warware kowacce matsala ce , maimakon yad inga yin amfani da ƙarfin soja don tsoratar da hukumomin gwamnati.

Haka dai ministan ya juya shi da tawagarsa suka wurin ala dole domin sojojin sun hana shi shiga filin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *